Amurka: Mahaukaciyar Guguwa Ta Halaka Mutum Hudu A Oklahoma, Ta Jikkata Sama Da 100

Oklahoma Tornado

Mahaukaciyar guguwar ta halaka mutum hudu a jihar Oklahoma da ke Amurka tare da barin dubbai da rashin wutar lantarki a Lahadin da ta gabata bayan barkewar wani mummunan yanayi da ya rusa wasu gine-gine a tsakiyar wani gari na karkara tare da raunata akalla mutum 100 a fadin jihar.

WASHINGTON, D. C. - Fiye da mutum 20,000 ne suke zaune babu da wutar lantarki bayan da guguwar ta fara a daren Asabar.

Oklahoma tornado

Barnar ta yi yawa a Sulphur, wani gari mai kusan yawan kusan mutum 5,000, inda guguwar ta ruguza gine-gine da dama a cikin garin, ta yi jifa da motoci da bas-bas tare da sassare rufin gidaje.

"Barnar da guguwar ta yi ba za ta misaltu ba," in ji Gwamnan Oklahoma Kevin Stitt yayin ziyarar da ya kai garin da ke fama da wahala. "Da alama guguwar ta lalata duk wasu wuraren kasuwanci da ke cikin gari."

Oklahoma

Stitt ya ce kimanin mutum 30 ne suka jikkata su kadai a cikin Sulphur, ciki har da wasu da ke cikin wata mashaya yayin da guguwar ta afka.

Asibitoci a fadin jihar sun ba da rahoton jikkatar kusan mutum 00, ciki har da mutanen da ga alama sun yanke daga faduwar tarkace ko suka ji rauni daga fadowa, a cewar Sashen Ba da Agajin Gaggawa na Oklahoma.

Mummunan yanayin na Oklahoma ya karu da dama da rahotannin guguwar da ta yi barna a tsakiyar kasar Amurka tun ranar Juma'a.

Oklahoma

A ranar Lahadin da ta gabata, hukumomi a Iowa sun ce wani mutum da ya ji rauni a lokacin wata guguwar da ta afkawa garin Minden ranar Juma'a ya mutu, a cewar rahotannin cikin gida.

Hukumomin kasar sun ce guguwar ta Sulfur ta fara ne a wani wurin shakatawa na birnin kafin ta bi ta cikin tsakiyar garin, inda ta karkata alkiblarta tare da yage rufi da bangon da aka gina da bulo.

Guguwar ta fasa tagogi da kofofi daga tsarin da ya rage na ginin a tsaye.

-AP