Mahaukaciyar guguwar Laura, wacce ta sauka a tekun jihar Louisiana ta Amurka mai karfi a mataki na 4, ta rage karfi, amma har yanzu tana da hadari sosai da kuma yuwuwar yin kisa.
Ya zuwa jiya Alhamis da rana, Laura ta sauka a tsakiyar gabashin garin Shreveport na jihar Louisina, tare da iska mai karfin tafiyar kilomita 100 a sa’a guda. Ana tsammanin tafka ruwan sama da zai kai santimita 46 a sassan jihohin Louisiana da Arkansas. Akwai kuma yuwuwar fuskantar mahaukaciyar guguwa.
Akalla mutane hudu ne aka bada rahoton sun mutu sakamakon guguwar. Fiye da mutum dubu 700,000 a jihohin Texas da Louisiana basu da wutar lantarki, kana ta lalata gidaje da dama da kuma shaguna.
Sai dai shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Amurka, Peter Gaynor, ya ce barnan da guguwar ta yi bata kai abin da aka yi tsammani ba.
A jiya Ahamis Gaynor da wasu jami'ai suka yi wa shugaban kasa Donald Trump bayani a hedkwatar FEMA da ke Washington. Tuni dai Trump ya ayyana dokar ta baci a jihohin Louisiana, Texas da Arkansas, kana ya ce yana shirin kai ziya a karshen wannan makon.
Facebook Forum