Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Umurci Jama'a Su Bar Matsugunnansu Yayin Da Mahaukaciyar Guguwar Ian Ke Kusantar Jihar Florida


Mazauna jihar Florida miliyan 2na ficewa daga gidajensu yayin da guguwar Ian ke gabatowa
Mazauna jihar Florida miliyan 2na ficewa daga gidajensu yayin da guguwar Ian ke gabatowa

Mazauna jihar Florida sama da miliyan biyu ne hukumomi suka ba umarnin su bar gidajensu yayin da guguwar Ian ke kusantar yankin.

Cibiyar sa ido kan guguwa ta Amurka da mazauninta ke birnin Miami ta ce mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da Ian tana kara karfi yayin da take kusantar jihar Florida da ke kudu maso gabashin Amurka.

Mahaukaciyar guguwa
Mahaukaciyar guguwa

Masu hasashen yanayi sun ce Ian na kusantar gabar tekun Florida tafe da iska mai gudun kilomita 250 a cikin sa'a guda, dab da gabar da zata zama mahaukaciyar guguwa a mataki na 5 a ma’aunin cibiyar, wanda shi ne mafi karfi.

An ga guguwar a tazarar kilomita 105 a yammaci da kudu maso yammacin birnin Naples na jihar Florida bayan da ta ratsa ta tsibiran yankin Florida da safiyar Laraba.

Wasu masu tserewa daga guguwar Ian a Cuba
Wasu masu tserewa daga guguwar Ian a Cuba

Mutane sama da miliyan biyu da ke zama a kusa da gabar tekun Florida daga yamma, aka ba umarnin ficewa daga gidajensu, yayin da Gwamna Ron DeSantis ya girke dubban dogarawan tsaron kasa a matsayin wani bangare na matakin da jihar ta dauka. Disney World, Universal Studios da SeaWorld, na daga cikin wuraren shakatawa da yawon bude ido da aka rufe.

XS
SM
MD
LG