WASHINGTON, D. C. - Masu hasashe sun ce guguwar ta haifar da ambaliya ruwa mai yawa kuma ta zubar da ruwan sama da ya kafa “tarihi”, wanda ya kai inci 25 (santimita 64) a kebabbun wurare.
"Barnar da ta haifar da muke gani babban bala'i ne," in ji Gwamna Pedro Pierluisi.
"Ina kira ga mutane da su zauna a gidajensu," in ji William Miranda Torres, Magajin garin Caguas da ke arewacin kasar, inda aka samu rahoton zaftarewar kasa, tare da ambaliyar ruwa mai tsanani da ya sa titin kwalta ya fashe ya kuma shiga cikin wani rami.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana dokar ta-baci a yankin na Amurka yayin da idon guguwar ya tunkari yankin kudu maso yammacin tsibirin.
-AP