Guguwar Ian wacce karfinta ya ragu bayan da ta ratsa jihar Florida, ta sake zama mahaukaciyar guguwa a cewar cibiyar da ke sa ido kan bala’in guguwa a Amurka.
Cibiyar ta ce guguwar ta nausa zuwa yankunan jihohin Carolina ta Kudu da ta Arewa da kuma Georgia.
A cewar cibiyar, guguwar na cike da hadarin zubar da ruwan sama da zai iya haifar da ambaliyar ruwa da ka iya yin barazana ga rayukan jama’a.
A ranar Juma’a aka yi hasashen guguwar ta Ian za ta isa Carolina ta Kudu, inda karfinta zai fi karkata zuwa tsakiyar jihohin Carolina ta Kudu da ta Arewa a daren Juma’a zuwa wayewar garin Asabar.
Gabanin ta nausa wadannan yankuna, guguwar ta Ian ta yi daidai da Florida, lamarin da ya kai ga shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da tallafin gwamnatin tarayya ga jihar don a sake gina ta.