Al'ummar Adamawa suna son shugaba Buhari bayan ya tattauna da shugaban Kamaru akan batutuwan da suka jibanci tsaro to ya kawo batun gina madatsar ruwa da Kamaru tayi akan kogin Binuwai wanda ya gurbata masu harkokin noma, sufuri da kasuwanci.
Kogin Binuwai dai ya ratsa cikin kasar Najeriya da kasar Kamaru. Biyo bayan gina madatsar ruwa da Kamaru tayi a shekarar 1983 harkokin noma da na sufuri da kasuwanci sun samu rauni ainun a jihar ta Adamawa.
Dr Umar Ardo yace kamata yayi shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari da gwamnan jihar Adamawa su sake waiwayar yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da kasar Kamaru kan yin anfani da albarkatun ruwan kogin na Binuwai ta yadda kasashen biyu zasu anfana..
Dr Ardo yace Kamru ta kare ruwan kogin daga inda ta gina madatsan ruwan saboda lokacin da suke yara suna ganin jiragen ruwa suna kawo kaya su sauke. Amma yanzu babu. Shi ma sarkin ruwan Gerio Malam Abdulrazak Abubakar yace alatilas da dama daga cikinsu sun rasa sana'o'insu sakamakon karancin ruwan kogin. Suna kira a dinga bude masu ruwa domin su samu walwalar komawa kamun kifi wadda ita ce sana'arsu.
Akwai kuma matsalar ambaliyar ruwa duk lokacin da madatsar ruwan . Lamarin kan sanya asarar rayuka da dukiyoyi da kuma anfanin gona.
Ga rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5