Wakilin Muryar Amurka Adamu El-Hikaya ya zanta da dan majalisar tarayya Ustaz Yunus Abubakar akan gayyatar da shugaban kasa yayi masu na ganawa dasu da misalin karfe biyar na yammacin yau agogon Najeriya.
Ustaz Yunusu yace ba shakka sun samu sakon gayyata daga ofishin hulda da manyan ma'aikata ko bakin gwamnati. Manufar ganawar ita ce tattaunawa akan abubuwan da zasu kawo cigaba. To amma a nasu harsashen suna ganin zai shigo da batun majalisun domin a sasanta akan abun da ake gani kamar rashin jittuwa.
A cewar Ustaz Yunus su a majalisar sun rigaya sun wuce wannan matsayi domin sun yi sulhu tsakaninsu. Sun tattauna sun cimma masalaha. Idan kiran shugaban kasar akan matsalar majalisun ne zasu fada masa sun riga sun daidaita.
Akan jita-jitar cewa watakila shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da na majalisar wakilai Yusuf Dogara zasu sauka ko a tsigesu sai Ustaz Yunus Abubakar yace magana ce kawai ta sokiburutsu a keyi. Inji Ustaz Yunus babu wanda ya isa ya ciresu domin ba nadasu aka yi ba. Su 'yan majalisa suka nadasu kuma sai an samu yaddar kashi biyu cikin uku na 'yan majalisun kana za'a iya ciresu. Ko shugaban jam'iyya bai isa ya ciresu ba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.