Amurka da Najeriya na cigaba da tattaunawa kan yadda za su habbaka huldar cinakayyarsu musamman ganin cewa yanzu Amurka ba ta bukatar man Najeriya sosai.
Da ya ke amsa tambayoyin Aliyu Mustaphan Sakkwato, Babban Sakataren a Ma’aikatar Cinakayya da Masana’antu Abdulkadir Abdulkadir ya ce cinakayya ce ta sakakkiyar mara za a yi da tsakanin Najeriya da Amurka, kuma batun ingancin abin da aka sarrafa da kuma da kuma saukin saye na kan gaba cikin abubuwan da za a yi la’akari da su a wannan tattaunawar.
Ya ba da misali da yadda Amurka ke son Najeriya ta rika sayen alkama a wurinta, amma kuma ita Najeriya na cewa ya kamata Amurka ta je Najeriya ta noma tare da kafa masana’antun sarrafa alkamar idan ta kama ma a rinka fitarwa kasashen waje ana sayarwa. Y ace har Koko ma Najeriya na tayinsa ma Amurka kuma ana kan tattaunawa akai.
Ya ce akwai kuma tattaunawar da ake kan yi game da bukatar kafa masana’antar kera motoci a Najerya amma Amurka na nuna shakku game da shin ko za a iya kera irin motocin da ta ke so a Najeriya har a rinka fitarwa kasashen waje. Sannan su na ganin motocin na iya tsada saboda wasu dalilai. Ya ce Najeriya ta kuma baiwa Amurka zabin hada hannu da Najeriya wajen kafa kamfanin kera motoci a Najeriya
Da Aliyu Mustaphan Sakkwato ya yi nuni da yadda Amurka ke daridari da batun saka jari a Najeriya saboda kaurin suna da Najeriya ta yi, sai Abdulkadir ya ce tuni aka bayyana ma Amurka irin matakan da ake daukawa don kare dukiyar masu saka jari a kasar.