Buhari wanda ya isa birnin Washington tun ranar Lahadi ya koma gida a jiya Laraba bayan da ya gana da shugaba Obama da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry kan batutwuan da suka shafi tsaro da tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa.
Baya ga shugabannin gwamnati da ya tattauna da su, Buhari ya gana da wasu manyan ‘yan kasuwar Amurka da cibiyoyin hada-hadar kudaden kasar bayan da ‘yan Najeriya mazauna kasar ta Amurka da ya zauna da su.
A na shi kiyasin, Dr M.K Hassan, Malami a jam’iar Pennsylvania da ke Amurkan, kwalliya ta biya kudin sabulu ganin irin tarba da kuma yarjeniyoyi da aka kulla tsakanin Amurka da Najeriya musamman a fannin tsaro.
“Ganin yadda dangantaka ta samu matsala tsakanin gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, wannan an yi masa maraba sosai, kuma Obama ya nuna mai cewa yana so lallai ya taimakawa Afrika ganin cewa shima ya kusa sauka.” In ji Dr Hassan.
A cewar Dr. Hassan, shugaba Obama ya lura cewa bayan an kammala zabe lami lafiya a Najeriya, ya gane cewa idan ya taimakawa Najeriya wacce ta fi kowace kasa yawan al’uma, kamar ya taimakawa Najeriya ne.
“Misali dangantakar Amurka da Najeriya zai yi tasiri sosai kamar mastalar tsaro da ake fama da ita idan Najeriya ta bi Amurka a hankali ta gane siyasar kasar, za ta samu taimako sosai.” In ji Hassan.
Ga karin bayani a hirar da Salihu Garba ya yi da Dr. M.K Hassan: