Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria yace rundunar hadin gwiwa na yaki da yan kungiyar Boko Haram zata fara aiki a karshen watan Yuli idan Allah ya yarda.
A wata hirar da Muryar Amirka tayi da shi, shugaba Buhari yace Nigeria ce zata jagoranci rundunar ta hadin gwiwa da zata kunshi sojojin kasashen Chadi da jamhuriyar Niger da kuma Benin. Yace sojojin zasu yi kokarin murkushe yan Boko Haram.
Shugaba Buhari yayi wannan furuci ne a yayin ziyarar kwanaki hudu daya kawo Amirka. A ranar Talata ya gana da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry kafin ya gana da wakilan Majalisar dokokin Amirka da kuma taron da yan Nigeria wadanda suke zaune anan Amirka.
A ranar Litinin shugaba Buhari ya gana da takwaransa na Amirka Barack Obama a fadar shugaban Amirka ta White House. Shugaba Obama ya yabawa zaben da aka yi Nigeria data jagoranci mika mulki farko bisa tubar democradiya tun karshen mulkin soja a 1999.
Shugaba Obama yace duniya ta shedi yadda aka canja mulkin cikin lumana. Ya kuma kara da cewa ya damu ainun akan irin barnar da yan kungiyar Boko Haram suke yi.
To amma yace yayi imanin cewa shugaba Buhari yana da tsarin murkushe yan Boko Haram.
Shugaba Buhari ya dare kan ragamar mulki tare da yin alkawarin aiwatar da canje canje, kuma cikin yan makon da hawansa kan mulki ya canja hafsoshin mayakan kasar.
A wani bayani da aka buga a jaridar Washington Post, shugaba Buhari yayi alkawarin yaki da yan Boko Haram da gudanar da mulki kamar yadda ya kamata da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Akwai kuma alamar cewa Amirka da Nigeria suna dokin inganta dangantaka a tsakaninsu.