Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram mai ta da kayar baya ke ci gaba da zama karfen kafa a Najeriyar, wanda lamari ne da zai mamaye tattaunawar kasashen biyu.
Ana sa ran Shugabannin biyu tare da mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, za su tattauna yadda za a samar da sauyi ga siyasa da tattalin arzikin Najeriya, da zimmar dakile matsalar cin hanci da rashawa a kasar.
Wanna ziyara, wacce zai kwashe kwanaki hudu yana yi, ta kasance ta farko tun bayan da Shugaba Buhari ya lashe zabe a watan Maris.
Fadar White House dai ta jaddada cewa, wannan ziyara wani mataki ne na karfafa dangantakar Amurkan da Najeriya.