Muryar Amurka ta zaga ta zanta da 'yan Najeriya akan ziyarar shugaban kasar Muhammad Buhari da ya kawo nan Amurka.
Wani Abdulkadiri Abbas daga Gombe ya godewa amurkawa da shugabansu Barack Obama saboda gwadawa Najeriya soyayya. Kullum ana jin maganar Najeriya a bakin shugaban Amurka. Yayi fatan soyayyar zata dore domin ya nuna ya taimakawa kasar akan harkar tsaro da dakile cin hanci da rashawa. Ya roki shugaba Obama ya taimaka a dawo da kudaden da yace wasu shugabannin Najeriya sun sace sun kuma boyesu a Amurka da wasu kasashe.Tunda shugaba Buhari ya nuna talakawa ne nashi ya kamata a taimaka masa.
Wata Hajiya Fatima daga Kaltungo na ganin shugaba Buhari ka iya cin nasara akan lamarin tsaro da kuma samo kudaden da aka sace. Idan yayi dace kasar Amurka na iya tabbatar an maido dasu domin jama'ar kasar su samu walwala su huta da talauci. Tana ganin Amurka zata iya taimakawa da tsaro saboda darutsan da suka koya a wasu kasashe.
Alhaji Umaru Ali Goro shugaban nakasassun jihar Gombe yace a matsayinsu na 'yan kasa suna zato za'a samu cigaba na wurin taimakawa tattalin arzikin Najeriya wanda ya tabarbare. Abu dake biye dashi shi ne begen da suke dashi cewa za'a shawo kan cin hanci da rashawa da taimakon Amurka saboda ita ta cigaba. Ana sace kudin al'umma kuma ba'a yiwa al'umma aiki. Ana kai kudin waje a boyesu. Amurka na iya dakile cigaba da yin hakan. Banda haka Amurka na iya gano barayin a kuma karbo kudin a yiwa kasa aiki dasu. Akwai karfin gwiwar samun ingancin tsaro lamarin da ya fi addabar arewa maso gabashin kasar.
Arewa maso gabashin Najeriya ta fi koina talauci na arziki da ilimi. Cikin marasa ilimi miliyan goma dake kasar miliyan biyar na arewa maso gabas ne. Kuma yankin ne rikicin Boko Haram ya fi daidaitawa.
Ga karin bayani.