Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Gayawa 'Yan Majalisun APC Su Mutunta Jam'iyya


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

A taron ganawa da 'yan majalisun APC a tarayya shugaba Buhari ya gaya masu su mutunta muradun jam'iyyar

Shugaban ya sake nanata kiran da ya yiwa 'yan majalisun APC kan su mutunta muradun jam'iyyarsu kodayake shi kansa bai fito fili ya bayyana abun da yake so ba a dambarwar shugabancin majalisun.

A ganawarsu da 'yan majalisun a dakin taron fadarsa, Buhari yace ya sa ran yadda 'yan Najeriya suka ba APC goyon baya haka 'yan majalisaun zasu ba jam'iyyarsu goyon baya, wato su yi muba'aya ga muradun jam'iyyar.

Dan majalisa Ustaz Abubakar ya yi karin haske inda yace saboda sun kada PDP kuma suna da yawa a majalisun sai shugaban ya dauki cewa komi zai tafi lami lafiya. To amma gashi wakin hula ya kai ga dare. Abun gaskiya bai ji dadi ba musamman yadda aka samu mataimakin shugaban majalisar dattijai ya kasance dan PDP.

Yace shugaban ya kirasu ne domin an ce ya dora to amma shi baya son doriya. Yana son a bi ka'ida. Yace lallai jam'iyya ce gaba amma yana rokonsu kowa ya danne burinsa ya mutunta muradun jam'iyya. APC ta fi kowa da kowa domin ta dalilinta suka ci zabe. Ya basu shawarar su gana da shugaban jam'iyyar ya basu shawara kuma kada a jisu a waje suna jayayya.

Shugaban jam'iyya ya tashi ya fadawa shugaban kasa cewa akwai matsaya wadda kakakin majalisa ya bashi amsa. Nan da awa hudu za'a gama shawara kuma za'a dawowa shugaban matsaya.

Wani dan majalisa yace dagewar mutun daya ya kawo matsala na cewa sai abun da yake so za'a yi wanda kuma ba zai yiwu ba..

Garahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG