Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Tare Da Yin Awon Gaba Da Matarsa A Kwara


Segun Aremu
Segun Aremu

Wasu mutane dauke da makamai sun harbe wani basaraken gargajiya, tare da yin garkuwa da matarsa da kuma wani mutum guda a yankin arewa maso tsakiyan Najeriya, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

WASHINGTON, D. C. - Maharan dai sun kai farmaki ne a fadar Segun Aremu, Janar din soja mai ritaya kuma basarke mai suna Olukoro na Koro a daren ranar Alhamis.

Ba a dai bayyana ko su waye ‘yan bindigar ba ko kuma masu neman kudin fansa ne.

Wannan sabon kisa da sace mutane ya zo ne kwanaki bayan masu fafutuka sun bukaci a kafa dokar ta baci domin shawo kan lamarin.

Wasu kungiyoyin farar hula 50 ne ke son shugaba Bola Tinubu ya yi wannan ikirari, inda aka ce sama da mutane 1,800 aka sace tun bayan hawansa mulki a watan Mayun da ya gabata.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake yin Allah wadai da kisan da aka yi wa Olukoro na Koro a jihar Kwara, a matsayin "rashin hankali, mai ban tsoro, kuma abin kyama", Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya sha alwashin kama wadanda suka aikata wannan laifin. 'Yan sanda kuma sun ce ana farautar mutanen.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG