Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Sojoji: Basaraken Da Ake Nema Ya Mika Kansa


Sarki Clement Ikolo
Sarki Clement Ikolo

Kasa da sa’a 24 bayan fitar da sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriya ta yi, basaraken, Clement Ikolo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Delta inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta a kudu maso kudancin Najeriya ta ce Sarkin Masarautar Ewu a jihar Delta, Clement Ikolo ya mika kansa ga rundunar a ranar Alhamis.

Ikolo wanda basarake ne a karamar hukumar Ughelli a jihar ta Delta, na daya daga cikin mutum takwas da Hedkwatar Tsaron Najeriya ta fitar da sanarwar tana neman su ruwa a jallo.

Mutanen sun hada da Farfesa. Ekpekpo Arthur, Andaowei Dennis Bakriri, Akevwru Daniel Omotegbo (Aka Amagben), Akata Malawa David, Sinclear Oliki; Clement Ikolo Oghenerukeywe; Reuben Baru da Igoli Ebi.

“Hotunan mutanen da ake nema game da hannu a kisan sojojin Najeriya 17 a Ukuama da ke karamar hukumar Ugheli ta kudu a jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris.” Sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriyar ta wallafa a ranar Alhamis a shafinta na Facebook ta ce, hade da hotunansu.

Daga cikin mutanen akwai maza bakwai da mace daya.

Sai dai kasa da sa’a 24 basarake Ikolo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Gidan talbijin din Channels ya ruwato cewa da misalin karfe 6:41 na yamma basaraken ya kai kansa ga 'yan sandan.

Jaridar Leadership ta ce Ikolo ya gana da manema labarai gabanin mika kansa inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.

A ranar 14 ga watan Maris wasu matasa suka halaka sojojin Najeriya 17 cikinsu har da manyan ofisoshi hudu a yankin Ukuama a jihar ta Delta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG