Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Iyalin Wani Basarake Bayan Da Suka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Taraba


Jana'izar wasu da aka kashe
Jana'izar wasu da aka kashe

Lamarin dai ya faru ne a yankin Mutum Biyu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu 'yan bindiga sun sace matan wani basarake biyu da 'ya'yansa shida, inda suka kashe matan da 'ya'ya biyar bayan da suka nemi kudin fansa ba a basu ba. Daya daga cikin 'ya'yan ya tsira bayan da aka harbe shi amma ya samu ya tsere.

Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da aukuwar lamarin a ta a bakin kakakinta SP Usman Abdullah. Ya kuma ce rundunar ta na iya kokarinta don ganin an kamo masu hannu a mummunan lamarin.

Wani dan garin Mutun Biyu wanda aka yi jana'izar gawarwakin a idonsa mai suna Aliyu Mutum Biyu, ya ce sun binne mutane bakwai a wuri guda saboda gawarwakin sun fara rubewa kafin a gano su.

Kwamanda Ahmad Muhammad, wanda ya jagoranci tawagar 'yan bangar da ta je dajin da aka dauko mutanen, ya shaida wa Muryar Amurka cewa sun ga harbin bindiga a jikin gawarwakin mutanen.

Ishiyaku Umaru Tammai, na daya daga cikin 'yan bangan da suka gano daya daga cikin 'ya'yan basaraken da ya tsira da ransa, ya ce a lokacin da suka ga yaron ba ya iya tafiya sai dai rarrafe kuma ya bayyana musu cewa masu garkuwan sun kashe sauran 'yan uwansa.

Saurari rahoton Salisu Lado:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG