Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Da Iyalinsa A Jihar Taraba


‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Ana ci gaba da samun mastalar rashin tsaro a Najeriya musamman a Arewa maso gabashin kasar inda wasu ‘yan bindiga suka kashe wani basarake a garin Modibbo da ke karamar hukumar Ardo Kola ta jihar Taraba.

TARABA, NIGERIA - ‘Yan bindigar sun yi garkuwa da dansa da matarsa, su ka kuma yi awon gaba da wasu mutanen da yawansu ya kai goma ciki, har da mata da yara - har da mai shayarwa, duk a garin na Mobibbo.

SP Usman Abdullahi Jada dake kakakin rudunar ‘yan sandan jihar Taraba shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin; ya kuma kara da cewa rudunarsu na yin dukkan mai yiwuwa domin ganin an kawo karshen yawan faruwar hare-haren a fadin jihar.

Samaila Isa Jauron ‘kani ga Jauron da aka kashe ya ce suna zaune da ‘ya’yansa sai su ka ji harbe-harbe a cikin gari, amma kafin su ankara sun riga sun iso kawai sai suka harbe ‘ya’yan shi wato Jauron Babaje, nan take sai ya mutu.

Shi ma an daure shi da matarsa amma daga baya sai suka sake shi da matarsa - su biyu ka dai suka tsira, wasu daga cikin mazauna garin sun koka sakamakon rashin kwanciyar hakali a yankin nasu baki daya musanman in dare ya yi, gaba dayansu watsewa su ke yi, inji Gidado jibirin

Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Garba:

‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Da Iyalinsa A Jihar Taraba.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG