Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake A Jihar Taraba


Yan bindiga
Yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun kashe sarki mai daraja ta uku Abdulmutallib Nuhu a gidansa da ke wajen garin sansanin karamar hukumar Gasol ta jihar Taraba.

TARABA, NIGERIA - Hassan Ibrahim sakataren sarkin ne ya shaidawa Muryar Amurka abin da ya faru da kuma yadda suka ji karar harbe-harbe a cikin gari bayan saduwar sa da sarkin.

Alhaji Iliyasu Galadiman Sansani na Gasol, ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a gidan sarkin inda yake karbar baki a yankin na Sansani, ya kuma yi kira ga al’ummar garin da su zauna lafiya.

Abdulahi Sa'adu, shugaban karamar hukumar Gasol ya ce yanzu haka suna gidan sarkin suna karbar gaisuwa da kuma shirye-shirye na yadda za'a yi jana’izar sarkin.

Yayin hada wannan rahoton, mun yi kokarin jin ta bakin ‘yan sadan jihar Taraba amma haka bata cimma ruwa ba, mun kuma aika da sako da kuma yi masu waya amma ba amsa.

Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Garba:

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake A Jihar Taraba.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG