Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Basarake A Jihar Kogi


Gwamna Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello

Baya ga basaraken da suka sace, ‘yan bindigar har ila yau sun yi garkuwa da wasu manyan fadawa biyu.

Wasu mahara sun sace Sarkin Aghara a karamar hukumar Kabba-Bunu da ke jihar Kogi a tsakiyar arewacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust da ta ruwaito labarin ta ce an kashe wata mata a fadar Sarki Pa David Obadofin yayin harin da ‘yan bindigar suka kai da sanyin safiyar Talata.

Baya ga Pa Obadofin da suka sace, ‘yan bindigar har ila yau sun yi garkuwa da wasu manyan fadawa biyu.

Bayanai sun yi nuni da cewa maharan sun fada farfajiyar fadar ne suna harbin kan mai uwa da wabi a lokacin da suka kai harin.

Rundunar ‘yan sanda jihar ta Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin tana mai cewa ta tura jami’anta don kubutar da mutanen tare da kama ‘yan bindigar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG