Kungiyar tayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan nemo daliban Chibok da aka sace su a makarantarsu ta sakandare a watan da ya wuce.
Shugaban kungiyar Auwal Babanliya, yace yakamata ‘yan Najeriya, su hada kai domin idan ba’a hada kai ba za’a cimma buri dakile masu tada kayar bay aba.
Mai shekaru saba’in da uku Mr. Dewa, bai gamsu da abubuwan dake faruwa a Najeriya bay ace” abunda ya fito dani shine abunda ya faru a Chibok, wani addini yace a kwashe ‘yan mata aje a siyardasu babu wani addini a duniya, Obangiji bai yardaba.”
Wata ‘yar asalin garin Gwoza dake jihar Borno Miss. Angelina, tafadi ra’ayinta dangane da rashin tsaro da ya addabi arewa maso gabashin Najeriya, tace"bamu iyayin barci bamu san abunda ake ciki ba tunda aka sace ‘yan mata bamu samu kwanciyar hankali ba."