Gwamnatin ta tara yara Musulmai da Kirista domin su yi addu'a ta musamman Ubangiji Ya sa a sako daliban da ake garkuwa da su. Gwamnatin jihar da shirin cire tallafin man fetur ko SURE-P suka dauki nauyin shiryawa da gudanar da addu'o'in.
Alhaji Hassan Nuhu babban daraktan shirin SURE-P ya yi karin bayani inda yace mai girma gwamnan jihar Dr. Muazu Babangida Aliyu yana ganin a ranar irin ta jiya a tara yara da manyan shugabannin addinai su yi addu'o'i na musamman domin Allah Ya kubutar da yaran da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su. Kuma haka aka yi inda aka sa yara Musulmai da Kirista suka yi addu'o'i.
Alhaji Shehu Haruna kwamishanan kula da harkokin addinai na jihar Neja ya bayyana dalilin sa yara su yi addua.Yace Allah yana karbar addu'ar yara domin basu da zunubi. Addu'ar ta neman Allah Ya taimaka yaran da aka sace su fito.
Batun cewa ko babu wata dabara da ta ragewa gwamnatin Najeriya sai komawa ga addu'a, Alhaji Ahmed Isa Ibeto mukaddashin gwamnan jihar wanda kuma shi ne ya karanta jawabin shugaban kasa Goodluck Jonathan yace gwamnati tana da dabaru amma kuma addinai sun nuna a roki Ubangiji.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.