Badeh, ya ce, "labari dai mai kyau ga iyayen 'yan matan shi ne mun san inda su ke, amma ba za mu iya gaya ma ku ba."
An sace 'yanmatan ne a tsakiyar watan Afrilu lokacin da su ke daukar jarabawa a wata makarantar sakandare da ke kyauyen Chibok da ke arewacin Nijeriya.
Mayakan sa kan kungiyar Boko Haram mai kaifin kishin Islama sun dau alhakin sace 'yan matan, kuma sun ce su na so a yi musayar 'yan matan da 'yan kungiyarsu da ke fursuna.
Kasashe da dama, ciki har da Amurka, na taimaka ma Nijeriya wajen neman 'yanmatan.