Zainab Maina ministan matan Najeriya tace bayan an gano daliban Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace za'a yi masu wani tanadin da za'a karfafasu domin su cigaba da iliminsu. Wadanda ma lamarin bai shafa ba su da iyayensu gwamnati zata karfafasu kada su karaya amma su cigaba da ilimi.
Tsohuwar minista Aishatu a ma'aikatar ilimi ta nuna matukar juyayi akan sace daliban Chibok. Tace ana tauyemasu hakki ana kuma tauyemasu ilimin 'ya'yansu mata. Koda a lokacin jahiliya idan ana yaki ba'a taba mata amma sai gashi yayin da ake daukaka ilimi an sace yara mata.
Hajiya Adama Ummi Dankwanbo ta karbi lambar yabo a madadin gwamnan jihar Gombe Dankwambo, jihar dake makwaftaka da jihohin dake cikin dokar ta baci. Hajiya Ummi tace lokacin da mijinta ya zama gwamna yace harakar ilimi zai fara sa gaba domin Gombe na daya daga cikin jihohin da suke baya a harkar ilimi. Amma yanzu idan an zagaya makarantu za'a ga irin aikin da gwamnan keyi.
To saidai kwamishanan yada labarai na jihar Kano Abubakar Danburam ya kushe tsarin gwamnatin tarayya akan ilimin tsangaya. Yace yayin da aka kebe almajirai gefe guda wato ana nufin su ba mutane ba ne. Ai ko mutane ne kamar kowa. Kamata yayi a kawosu cikin jama'a da wani tsari da zasu bi su san cewa daidai suke da kowa.
Ita dai Mujallar Tozali da Maimuna Yaya Abubakar ke wallafawa tana shirya irin wannan taron ne kowace shekara.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.