Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasiyar Shugaban Kungiyar al-Qaida Osama Bin Laden


Osama bin Laden
Osama bin Laden

Marigayi shugaban al-Qaida, mutumin da ya bayar da umarnin kan harin da aka kai Amurka a shekara ta 2001, wanda ya halaka mutane kusan dubu 3, cikin wasiyyarsa yace dukiyarsa dala Miliyan 29, yana so a yi amfani da galibin kudin wajen jihadi don Allah.
Jiya Talata ne Amurka ta bayyana wasiyyar a zaman wani bangare na kasidu da bayanai 113, data kama a gidan da yake da zama a Abbottabad na Pakistan, lokacin da sojojin Amurka na musamman, suka kai masa farmaki kusan shekaru biyar da suka wuce.
Kasidun da aka rubuta da larabci, aka fassara kuma hukumomin ayyukan leken asirin Amurka suka bayyanawa duniya, shine kashi na biyu a jerin takardun da wadannan sojoji suka dauko daga mabuyar shi Osama Bin Laden, inda yake zaune da matansa da kuma yara.

XS
SM
MD
LG