Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Kera Motoccin "Lamborghini" Ya Kaddamar Da Motar 2016


Motar 2016
Motar 2016

Shahararren kamfanin kera motocin nan “Lamborghini Centenario” sun yi bukin kaddamar da sabuwar motar su da suka kira "Limited-Production 751-HP" ta shekarar 2016, a babban birnin Geneva na kasar Switzerland. An dai kaddamar da sabuwar motar ne a dai-dai lokacin da ake bukin cikar shekaru 100 da haihuwa makirkirin kamfanin, Mr. Ferruccio Lamborghini, wanda ya mutu a shekarar 1993, dan asalin kasar Italy.

An kiyasata kudin motar da suka kai dallar Amurka milliyan $1.9M dai-dai da kudin Najeriya naira milliyan dari ukku da tamanin N380,000,000. Kamfanin dai zasu sake kera irinta guda 20, a nan gaba. Motar nada karfin injin V-12 dai-dai da karfin dawakai 5, kana anyi mata tsari iri na motar zamani da bata da shan mai ga kuma dankaran gudu. An kiyasta gudun ta da cewar zatayi tafiya daga nisan kamar Abuja zuwa Kano cikin awa daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG