Kamfanin fasaha Apple yana shirin gayawa kwamitin majalisar dokokin Amurka yau Talata cewa, bukatar da hukumomin tsaron kasar suka gabatar na bude wayar da daya daga cikin wadanda suka kai harin ta’addanci a San Benardino, California da ya kashe mutane goma sha hudu, ‘zai bude wata dama mai hatsarin gaske da gwamnati zata rika yiwa mutane kutse a rayuwarsu.
A cikin shaidar da ya rubuta da aka riga aka fitar, babban lauyan kamfanin Apple Burce Sewell yace, kirkiro da wata manhaja da zata sa a iya bude wayar Syed Rizwan Farook zata jefa miliyoyin na’urorin Apple da ake sayarwa a duk fadin duniya cikin hadarin tsaro.
Sewell yace, kirkiro da manhajar ba waya daya kawai zata shafa ba, zata raunata tsaron dukansu, dukanmu zamu amince da cewa, ba batun bude waya daya ake yi ba.
Babbar hukumarr binciken Amurka FBI, ta bukaci kamfanin apple ya kirkiro wata manhajar da zata hukumar damar bincikawa taga ko Farook, wani Musulmi haifaffen Amurka, ya yi Magana da wadansu dangane da harin da suka kai farkon watan Disamba da matarshi haifaffar kasar Pakistan, Tashfeen Malik. An kashe dukansu biyu ‘yan sa’oi da kai harin a wata musayar wuta da ‘yan sanda.
Wata kotun majestire a California ta umarci kamfanin Apple ya yi biyayya da bukatar da hukumomi suka gabatar, sai dai babu tabbacin abinda zai biyo bayan daukaka karar da kamfanin na Apple ya shigar.
Jiya litinin wata kotu dabam a birnin NY ta yanke hukumci cewa, ma’aikatar tsaro ba zata iya tilastawa kamfanin ya bi umarnin ba.
Idan kotun daukaka karar tayi na’am da umarnin da hukumcin da alkali ya yanke a California, wadansu jami’an tsaro sun ce, zasu bukaci kamfanin na Apple ya bude wadansu wayoyi da ake gudanar da bincike da suka shafi aikata laifuka.