Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Binciken Ra'ayoyin Jama'a Game Da Yan Takarar Amurka


Wani sabon binciken ra’ayoyin jama’a ya nuna hanshakin dan kasuwar nan Donald Trump yana kan gaba tsakanin ‘yan takarar dake neman jam’iyarsu ta Republican ta tsaidasu takarar shugaban kasa, yayin da tsohuwar sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton take gaba a jam’iyar Democrat.

Binciken ra’ayoyin jama’an da CNN da kuma ORC suka gudanar ya nuna Trump yana da goyon bayan kashi 49%. Fiye da sauran abokan takararshi idan aka hada goyon bayan da suke da shi baki daya. Wanda ke biye da shi na kurkusa shine saneta Marco Rubio wanda yake da kashi 16% sai senata Ted Cruz da kashi 15%.

A takarar jam’iyar Democrat kuma, binciken ra’ayoyin jama’a ya nuna Clinton babbar jami’ar diplomasiyar Amurka tsakanin shekara ta dubu da dari tara zuwa dubu biyu da goma sha uku, ta ba abokin takararta daga jihar Vermont mai ra’ayin sassauci Bernie Sandres rata inda take da kashi hamsin da biyar cikin dari yana da kashi talatin da takwas.

Yau talata ne jam’iyun zasu gudanar da zabe a jihohi goma sha daya da ya kasance ranar zabe mafi girma cikin wata guda da aka shafe kawo yanzu ana matsanancin yakin neman zabe. Binciken ya nuna cewa, Trump na rinjaye a jihohi goma a zaben na yau da ake kira “Super Tuesday”, Trump yana da goyon baya a dukan jihohin banda jihar Texas inda Cruz yake kyautata zaton lashe zabe a jihar da ya fito.

Bisa ga dukkan alamu kuma, Clinton zata ci zabe a galibin jihohin da take takara da Sanders, wanda a yakin yakin neman zabensa tare da kushewa gibin dake tsakanin attajirai da talakawa, da kuma manyan kamfanoni.

XS
SM
MD
LG