Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da Suka Fi Arziki A Duniya


Mujallar Forbes ta wallafa jerin sunayen manyan attajiran duniya na shekarar nan ta 2016.

Bill Gates, mai kamfani Microsoft shine a kan gaba, mujallar tayi kiyasin cewa dukiyarsa za ta kai dala bilayan 75.

Da ga nan kuma sai, Amanicio Ortega, mai kamfanin tufafin da ake kira Zara na kasar Spain, shi kuma ya na da dukiyar da ta kai dala biliyan 67.

Shi kuma Warren Buffet, shahararren mai sana’ar hannun, jari shi ya zo na uku da dukiyar dala biliyan 60.8.

Mace mafi arziki a cikin jerin sunayen ita ce Liliane Bettencourt mai kamfanin kayan kwalliyar L’Oreal, ita kuma ta na da dala biliyan 36.1

Alhaji Aliko Dangote, shi kuma an yi kiyasin dukiyarsa za ta kai dala biliyan 15.4, shi ya zo na 51 cikin jerin sunayen.

Matashi mafi karancin shekaru a jerin sunayen shi ne Alexandre Andersen dan kasar Norway, mai shekaru 19 da haihuwa. dukiyarsa da ta kai dala biliyan 1.2. Shine na 1,476 a jerin sunayen.

Wanda kuma ya fi yawan shekaru shi ne David Rockefeller, Sr. mai shekaru 100 a duniya, arzikinsa ta hanyar Mai da kuma aikin banki ne. An yi kiyasin dukiyarsa ta kai dala biliyan 3, shi ya zo na 569 a jerin mutanen.

Wannan shi ne karo na 30 da mujallar ta fidda sunayen mutanen da su ka fi arziki a duniya.

A shekarar nan masu biliyoyin dala ba su da yawa, in aka danganta da bara a cewar mujallar.

Har yanzu Amurka ce kan gaba a jerin kasashe masu mutanen da ke da biliyoyin daloli, amma kuma China ta sami karin mutane 70 a jerin mutanen bana.

XS
SM
MD
LG