Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zasu Ziyarci Kasashen Afirka Biyar A Kan Babur


Kungiyar mata matasa masu tuka babur/mashin wadda ake kira Amazon Motorcycle club na shirin tafiya zuwa kasashen Afika guda biyar akan mashin domin halartar bikin ranar mata ta duniya na shekarar 2016.

Matan zasu kama hanya zuwa kasashen nahiyar Afirka biyar ne a ranar litini 4 ga watan Maris daga birnin Lagas, kuma za’a ga matan akan mashinan su a hanyoyin legas zuwa makwabciyar kasar wato Benin, daga can sai Togo, zuwa Ghana sai Ivory Cost inda zasu halarci taron mata na duniya da za’a gudanar a ranar 8 ga wannana watan a kasar ta Ivory Cost.

Wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar masu tuka mashinan da suka sami zantawa da mujallar Vanguard a birnin Legas sun hada da injiniya kuma babbar ‘yar kasuwa mai suna Otaru, da wata lauya mai suna Utibe Abasi Nkango kuma sun bayyana cewa zasu kwashe kwanaki hudu kafin su isa kasar ta Ivory Cost.

Matan sun bayyana cewa zasu dawo jahar Legas ranar 14 ga watan maris, kuma babban makasudin abin da wannan kungiya ta mata matuka manyan mashina ke son cima sun hada da karfafa mata, da ba mata manoma iri kyauta domin bunkasa harkokin noma, da kuma jan kunne da gargadi musamman ga direbobi domin tuka ababen hawa cikin aminci da kiyayewa.

Sun kara da cewa sun ji labarin mashin na daya daga cikin ababen hawa da aka fi anfani da shi a kasar ta Ivory Cost, dan haka matan sun bukaci takwarorin su maza matuka manyan mashina irin nasu domin yi masu rakiya, da kuma gayyatar irin kungiyar dake can kasar domin su tarb su a hanya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG