Wasu matasan billoniyoyi a duniya da kuma shekarun su a dai-dai lokacin da suka samu kudin su. Mark Zuckerberg, a shekarar 2006 ya mallaki kimanin dallar Amurka milliyan $1M a asusun ajiyan shi na banki, a lokacin da yake dan shekaru 22. Wannan matashi shine shugaban kamfanin zumunta na facebook. Ya zama karamin billoniya a duniya da ya mallaki kimanin $43.9B a yanzu haka.
Evan Spiegel, tun yana dan shekaru 23, koda ya zama milloniya, shine shugaba kuma ma kirkirin shafin zumunta na “Snapchat” a shekarar 2013. Kodai da ya kai shekaru 25, ya mallaki sama da billiyan $1B wanda ya zama matashi da ya samar ma kanshi kudi batare da taimakon wani ba, yanzu haka yanada sama da billiyan $2.1B.
Richard Branson, tun yana dan shekaru 23, ya fara samun kudin shi, a shekarar 1973. Shine mai kamfanin “Virgin Group” wanda yake da kamfanoni a karkashin wannan suna, da suka haka da kamfanin jiragen sama da na sadarwa. Yanzu dai dan shekaru 41, dai yana da adadin kudi da suka haura sama da billiyan $5.1B.