Duk dai da cewar tattalin arzikin duniya ya shiga cikin wasu manyan lokaci, wanda hakan yasa masu kudi a duniya sun ji wannan girgizar. Domin kuwa tun a shekarar 2009 ba’a kara samun raguwar masu kudi a jerin sunayen masu kudi na duniya ba. Amma a wannan shekarar cikin jerin masu kudi a duniya, yawan su ya ragu daga 1,826 zuwa 1,810, a takaice an samu mutun 16 da suka sauka daga layin masu kudi.
Mutun na farko da yafi kowa kudi a duniya shine Bill Gates, mai kamfani kwamfuta na “Microsoft” ya nada shekaru 60 da haihuwa, ya mallaki dallar Amurka billiyan $75B, kuma shine na farko wanda ya rike kambun mai kudin duniya na tsawon shekaru 3 a jere.
Na biyu kuwa shine Amancio Ortega, dan kasar Spain mai shekaru 79 da haihuwa, ya kuma mallaki kimanin dallar Amurka billiyan $67B. Mafi akasarin kudin shi daga sana’ar gidaje da filaye ne a kasashen duniya. Na uku kuwa shine Warren Buffett, wanda ke da shekaru 85 a duniya, ya mallaki kimanin dallar Amurka billiyan $60.8B. Kamfanin shi mai suna “Berkshire Hathaway” wanda ya zama kamfani na 5 da ake takama da su akasar Amurka. Yana kuma da hannun jari a kamfanoni kamar su bankin Wells Fargo, IBM, Coca-cola da dai sauran su.
Na hudu kuwa shine Carlos Slim Helu, dan kasar Mexico, mai shekaru 76, yana da kimanin dallar Amurka billiyan $50B an kuma bayyanar da shi a matsayin mai kudin da ya fikowane asara, domin kuwa yayi asarar sama da billiyan $27.1B a tsawon shekarar da ta gabata. Mafi akasarin kudin shi daga sana’ar sadarwa ne. Na biyar kuwa shine Jeff Bezos, mai shekaru 52 a duniya, shi ke da kamfanin Amazon, yana da kimanin kudi da suka kai dallar Amurka billiyan $45.2B.
Zamu kawo muku sauran mutun 5 masu kudin duniya gobe idan Allah ya kaimu.