A ranar Lahadi, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kai ziyarar wuni guda a Jamhuriyar Nijar, a ci gaba da rangadin da ya kaddamar a kasashen kungiyar AES da nufin karfafa hulda a fannonin da suka hada da diflomasiya, tattalin arziki, yaki da ta'addanci da sauransu.