Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juyin Mulki: Tawagar ECOWAS Ta Sauka Nijar Domin Tattaunawa


Firai Ministan Rikon Kwarya Na Nijar Ali Mahaman Zeine Da Janar Abdulsalam Abubabakar Yayin Ziyara Zuwa Nijar
Firai Ministan Rikon Kwarya Na Nijar Ali Mahaman Zeine Da Janar Abdulsalam Abubabakar Yayin Ziyara Zuwa Nijar

Wannan tawagar ta je Jamhuriyar Nijar ne karo na biyu da nufin tantaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Tawagar wakilan kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka CEDEAO ko ECOWAS a karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalam Abubakar ta sauka birnin Yamai da ke Jamhuriyar Nijar a wannan Asabar.

Wannan tawagar dai ta je Nijar ne da nufin tantaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Firai Ministan Rikon Kwarya Na Nijar Ali Mahaman Zeine Ya Tarbi Tawagar ECOWAS Karkashin Jagorancon Janar Abdulsalam Abubabakar
Firai Ministan Rikon Kwarya Na Nijar Ali Mahaman Zeine Ya Tarbi Tawagar ECOWAS Karkashin Jagorancon Janar Abdulsalam Abubabakar

Wannan ne karo na biyu da tawagar a karkashin jagorancin Abdussalami Abubakar ta ke zuwa Nijar din tun bayan juyin mulki, kasancewar a ziyarar da suka kai kwanaki kalilan bayan juyin mulkin, ba su sami ganin jagororin juyin mulkin ba, hasali ma ziyarar ta su ta tsaya ne kawai a filin jirgin saman Yamai, ba tare ko shiga cikin birnin ba.

Daga bisani ne gwamnatin mulkin sojin ta ba da hakurin rashin karbar wakilan na ECOWAS, tana mai ambatar tsaro a matsayin dalilin daukar matakin.

To amma a wannan karon ana sa ran tawagar za ta yi ido biyu tare da tattaunawa da shugaban mulkin soji Abdourahamane Tchiani, su kuma ziyarci hambararen shugaban kasar ta Nijar Mohamed Bazoum da iyalinsa inda suke tsare yau kusan makwanni 4.

Fira Ministan rikon kwarya Ali Mahamane Lamine Zeine ne ya tarbi wannan tawwaga kafin ta gana da shugaban majalisar CNSP ta sojoji wato Janar Abdourahamane Tchiani.

Firai Ministan Rikon Kwarya Na Nijar Ali Mahaman Zeine Ya Tarbi Tawagar ECOWAS Karkashin Jagorancon Janar Abdulsalam Abubakar
Firai Ministan Rikon Kwarya Na Nijar Ali Mahaman Zeine Ya Tarbi Tawagar ECOWAS Karkashin Jagorancon Janar Abdulsalam Abubakar

Kungiyar ECOWAS wacce ta yi tir da juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli, ta lashi takobin maida shugaba Bazoum a kan mukaminsa wa lau ta hanyar sulhu ko da karfin soja.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG