Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juyin Mulki: ‘Yan Nijar Na Tayin Kafa Rundunar ‘Yan Sa- Kai Don Tallafawa Dakarun Kasar


 ‘Yan Nijar Na Tayin Kafa Rundunar ‘Yan Sa- Kai Don Tallafawa Dakarun Kasar
‘Yan Nijar Na Tayin Kafa Rundunar ‘Yan Sa- Kai Don Tallafawa Dakarun Kasar

Al'ummar kasar Nijar na shirye-shiryen yiwuwar fuskantar mamaya daga dakarun kasashen yankin kasashen ECOWAS.

WASHINGTON, D.C. - Hakan na zuwa ne makonni uku bayan da wasu sojoji masu ta da kayar baya suka hambarar da zababben Shugaban kasar da aka zaba bisa tsarin dimokradiyya.

Mazauna Yamai babban birnin kasar na yin kira da a dauki sojin sa-kai da za su taimaka wa sojoji a yayin da ake kara fuskantar barazanar kungiyar ECOWAS da ke yankin yammacin Afirka.

‘Yan Nijar Na Tayin Kafa Rundunar ‘Yan Sa- Kai Don Tallafawa Dakarun Kasar
‘Yan Nijar Na Tayin Kafa Rundunar ‘Yan Sa- Kai Don Tallafawa Dakarun Kasar

Kungiyar ECOWAS ta yi barazanar daukan matakin soji akan dakarun kasar da suka yi juyin mulki muddin ba su maido da mulkin farar hula da sakin Shugaba Mohamed Bazoum ba.

Ta kuma umurci dakarunta “masu jiran kar-ta-kwana” da su zauna cikin shiri domin dawo da zaman lafiya a Nijar bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi watsi da wa’adin da aka ba ta.

Shirin wanda wasu gungun mazauna birnin Yamai ke jagoranta, na da nufin daukar dubun-dubatar masu aikin sa-kai daga sassa daban-daban na kasar domin yin rajistar masu aikin sa-kai na tsaron Nijar.

Kungiyar za ta yi yaki, ta taimaka wajen kula da lafiya, da kuma samar da dabaru da injiniyoyi da sauran ayyuka, idan har gwamnatin mulkin sojan za ta bukaci taimako, kamar yadda Amsarou Bako, daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ranar Talata.

“Al’amari ne mai yuwa. Muna bukatar mu kasance cikin shiri a duk lokacin da abin ya faru,” Bako ya ce.

A ranar Asabar ne za a kaddamar da shirin daukar ma’aikata a birnin Yamai da kuma garuruwan da dakarun za su iya shiga, kamar kusa da kan iyakokin Najeriya da Benin, kasashen biyu da suka ce za su shiga tsakani.

Duk wanda ya haura shekaru 18 zai iya yin rajista kuma za a ba da jerin sunayen ga gwamnatin mulkin soja don kiran mutane idan ana bukatarsu, in ji Bako.

Gwamnatin mulkin soja dai ba ta da hannu amma tana sane da shirin, in ji shi.

Rikicin yankin na kara ta'azzara ne yayin da takaddamar da ke tsakanin Nijar da ECOWAS ke nuni da cewa babu wata alama da za ta lafa, duk kuwa da alamun da bangarorin biyu suka yi na cewa a shirye suke su warware rikicin cikin lumana.

A makon da ya gabata ne gwamnatin mulkin sojan kasar ta ce a shirye ta ke ta tattaunawa da ECOWAS bayan ta yi fatali da kokarin da kungiyar ta yi a tattaunawar, amma jim kadan bayan haka ta tuhumi Bazoum da "babban cin amanar kasa" tare da kiran jakadanta daga makwabciyarta Ivory Coast.

Ana sa ran manyan hafsoshin tsaron ECOWAS za su gana a wannan makon a karon farko tun bayan da kungiyar ta sanar da shirin aikawa da dakaru masu “zama cikin shirin kar-ta-kwana”.

Ba a san lokacin da rundunar za ta kai mamaya ba, amma mai yiwuwa za ta hada da dubban dakaru da dama kuma za ta haifar da mummunan sakamako, in ji masana rikice-rikice.

Mucahid Durmaz, babban manazarci a Verisk Maplecroft, wani kamfanin leken asiri na kasa da kasa, ya ce, "shigar da sojoji a iyakokin na iya haifar da yaki a yankin, tare da mummunan sakamako ga babban yankin Sahel da dama ke fama da rashin tsaro da talauci."

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG