Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Juyin Mulki Ya Shafi Daruruwan Daliban Nijar Masu Shirin Zuwa Karatu Faransa


Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron

Daruruwan daliban Jamhuriyar Nijar da ke fatan shiga jami’oin Faransa sun fada halin zullumi sakamakon rashin samun takardar biza bayan da gwamnatin Faransar ta rufe ofishin jakadancinta a birnin Yamai sanadiyyar yanayin siyasar da aka shiga a kasar.

NIAMEY, NIGER - Tun a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 ne kasar Faransa ta rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Yamai bayan da wasu masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka hambarar da zababben Shugaba Mohamed Bazoum, suka afkawa ofishin jakadancin Faransar.

Mutane sun kai harin ne da nufin yin tir da abin da suka kira shisshigin da ta ke yi wa al’amuran cikin kasar a kokarinta na ci gaba da yi wa kasar mulkin mallaka.

Sai dai makonni uku bayan faruwar wannan al’amari daruruwan daliban da suka sami gurbin karatu a jamio’in Faransar sun fada halin damuwa sakamakon rashin samun takardar biza kamar yadda Shugaban kungiyar ‘yan Nijar mazauna Faransa Adam Oumarou ya fadawa Muryar Amurka.

Kungiyar dalibai ta kasa wato USN a cewar kakakinta Mouloul Effred Alassan, na bin diddigin wannan al’amari don samar da mafita ga makomar wadanan daruruwan dalibai da ke cikin halin kila wa kala sanadiyyar tsamin dangantakar Faransa da Nijar.

Matakin rufe iyakokin Nijar da kungiyar CEDEAO ta dauka a wani bangare na jerin takunkumin da ta kakaba wa kasar bayan da soja suka yi juyin mulki da matakin rufe sararin samaniyar da Majalisar CNSP ta dauka don dakile dukkan wani yunkurin kai farmaki kan Shugabanin juyin mulkin abubuwa ne da manazarta ke ganin idan aka ci gaba da tafiya a haka ka iya shafar sha’anin karatun daliban kasar da ke jami’oin kasashen waje.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Yadda Juyin Mulki Ya Shafi Daruruwan Daliban Nijar Masu Shirin Zuwa Karatu Faransa. mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG