Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN AMURKA: Ba Za A Iya Kiyasta Illolin Da Takunkumin Taliban Ya Yi Wa Mata Da 'Yan Mata Ba - Ambassador Wood


Ambassador Robert Wood
Ambassador Robert Wood

A cewar rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da dama, halin jin kai a Afganistan yana da muni. Fiye da kashi 50 cikin 100 na al'ummar kasar kimanın mutane miliyan 23.7 na bukatar agajin jin kai.

Haka kuma Kusan yara miliyan 3 na fuskantar matsananciyar yunwa.

Sannan a watan Afrilu da Mayu, kimanin mutane 120,000 ne ambaliyar ruwa da zabtarewar laka ta shafa, wadanda suka lalata kauyuka tare da kashe mutane sama da 340.

Ana tsammanin Watakila wannan ne dalilin da ya sa Taliban ta amsa goron gayyatar halartar taro na uku da Majalisar Dinkin Duniya ta kira na jakadu na musamman kan Afghanistan, wanda zai gudana a birnin Doha na Qatar a ranakun 30 ga watan Yuni da 1 ga watan Yuli.

Daga cikin batutuwan da za a tattauna a Doha, akwai rikice-rikice da yawa a Afghanistan da kuma yadda 'yan Taliban ke murkushe 'yancin mata.

Mata a Afghan
Mata a Afghan

A cewar rahoton na Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, matan Afganistan suna fuskantar hukunce-hukunce, da tsare-tsaren dake nuna bambancin jinsi da cin zali akan şu.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Robert Wood ya ce, "Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya daban-daban da hukumomi masu zaman kansu yanzu suna kira ga tsarin take hakkin dan Adam na kungiyar Taliban ta ke yi."

Wadannan rahotanni sun bayyana dalla-dalla, kokarin da Taliban ke yi don kawar da mata daga cikin al'umma; zaluntar jinsi; rashin kulawa ga masu nakasa; da kuma take hakkin dan adam akan ƴan kabilu, addini, tsirarun harsuna, da kuma kungiyar LGBTQI+.”

Ambassador Wood Ya ce, "Dole ne kasashen duniya su ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Afganistan - musamman mata, 'yan mata, da kuma mambobin al'ummomin da aka sani.

Yuni 14th, 2024 kwanaki 1000 tun da Taliban ta hana yara mata zuwa makarantar sakandare a Afghanistan
Yuni 14th, 2024 kwanaki 1000 tun da Taliban ta hana yara mata zuwa makarantar sakandare a Afghanistan

Ambassador Wood ya kara da cewa “Dole ne mu nace mu canza wadannan matakan na zalunci; tukurawa don tabbatar da adalci da kuma yin la'akari da cin zarafi; da kuma fayyace cewa ba za a iya yin shiru ko kuma tauye hakkin dan Adam ba."

A Afghanistan, an hana 'yan mata zuwa makaranta sama da aji na 6

Ambasada Wood ya ce: "Ba za a iya kiyasta illolin da takunkumin na Taliban ya yi wa mata da 'yan mata ba.

A halin yanzu fiye da kwanaki 1,000 ke nan tun bayan da Taliban ta hana ‘yan mata shiga makarantun sakandare. Idan aka bar ire-iren wadannan takunkumin suka ci gaba, illar da za ta shafi 'yan Afganistan daga ko'ina cikin kasar shekaru da yawa masu zuwa tana da yawa."

Ambasada Wood ya ce "Dole ne mu tabbatar da cewa mata da masu shiga kungiyoyin farar hula suna da murya a Doha." "Dole ne a bayyana damuwarsu da dukkan shawarwari kan makomar Afghanistan."

Wannan sharhi ne na gwamnatin Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG