Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN GWAMNATIN AMURKA: Dole China Ta Saki ‘Dan Fafutukar Kare Hakkin Bil Adama Na Uighur Ilham Tohti


Ilham Tohti, Beijing, China, Feb. 4, 2013.
Ilham Tohti, Beijing, China, Feb. 4, 2013.

A wannan watan ne aka cika shekara goma da tsare mai fafutukar kare hakkin ‘dan Adam ta Uighur Ilham Tohti. Tohti wanda ya kasancewa har yanzu a tsare don kawai ya na neman hakkin 'yan Uighurs da sauran tsirarun kungiyoyi dake People’s Republic of China, ko PRC.

WASHINGTON, D. C. - Hukuncin daurin rai da rai da aka yi masa ya nuna kokarin da PRC ke yi na rufe bakin masu jajircewa don nuna adawa da ayyukan gwamnatin kasar na nuna wariya da sauran abubuwan cin zarafin bil adama, wadanda suka hada da kisan kiyashi da cin zarafin bil adama a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na Uighur.

Wani malami da ake girmamawa a kasar Sin, Ilham Tohti farfesa a fannin tattalin arziki a jami'ar Central dake birnin Beijing. Ya yi aiki shekaru da yawa don inganta dangantaka tsakanin 'yan kabilar Uighur da na Han Sinawa. Ya yi watsi da rarrabuwar kawuna da tashe-tashen hankula tare da kokarin daidaita sabanin da ke tsakanin wadannan kabilu. 'Yan kabilar Uighur wadanda galibinsu Musulmi ne na asalin Turkawa, sun fuskanci wariya sosai a yankin Xinjiang na kabilar Uighur mai cin gashin kansa.

A cikin rubuce-rubucensa, Tohti ya bayyana manufofin gwamnati da suka hana amfani da harshen Uighur, suna tauye wa Uighurs damar yin addininsu, da iyakance damarsu ta samun aikin yi, da kuma kwadaitar da hanin yin hijira zuwa yankin wadanda dukkansu ke haifar da rikicin kabilanci. Tohti shi ne ya kafa, kuma darektan gidan yanar gizon "Uighur Online," wanda ya ba da rahoto kan take hakkin ‘dan Adam ba wai kawai 'yan kabilar Uighur ba har ma da 'yan kabilar Han na kasar Sin.

A ranar 15 ga Janairu, 2014, 'yan sanda suka dauke Ilham Tohti daga gidansa da ke birnin Beijing. Tsawon watanni biyar ana tsare da shi ba tare daikon ganin kowa ba. A ranar 23 ga Satumba, bayan shari'ar rashin adalci, an yanke masa hukumcin daurin rai da rai kan zargin "yada wariya".

Turkey Uighur - Zanga-zangır Lumana
Turkey Uighur - Zanga-zangır Lumana

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi kiyasin cewa, sama da 'yan kabilar Uighur miliyan 1 da sauran kananan kabilun Musulmi mafi yawansu aka tara a sansanonin 'yan gudun hijira a yankin Xinjiang da ke Arewa maso yammacin kasar. Da farko China ta musanta wanzuwar sansanonin, amma yanzu ta ce ai "makarantun koyar da sana'o'i ne" wadanda suka zama wajibi don yaki da ta'addanci.

Kasar Amurka ta sake yin Allah wadai da irin ta'asar da PRC ke ci gaba da yi a jihar Xinjiang, tare da yin kira ga PRC da ta mutunta 'yan tsirarun kabilu da addinai, da gaggauta sakin Tohti da duk wadanda ake tsare da su ba bisa ka'ida ba a garin Xinjiang da ma daukacin kasar Sin ba tare da wani sharadi ba.

Wannan shine sharhi na ra’ayoyin gwamnatin Amurka

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG