Wuraren sun hada da cibiyoyin ba da umarni da sadarwa kan halin da ake ciki, rokoki, makamai masu linzami, jiragen sama marasa matuka, rumbunan ajiya, da wasu cibiyoyin makamai.
Bayan da aka kashe sojojin Amurka uku a lokacin wani hari da aka kai kan wani sansani a Jordan, shugaba Joe Biden ya ba da izinin kai hare-haren kan cibiyoyi da makaman da dakarun IRGC da kungiyoyi masu alaka da su ke amfani da su.
A ranar 7 ga watan Fabrairu, martanin da aka kai ya kuma yi sanadin mutuwar wani kwamandan kungiyar Kata’ib Hezbollah a Bagadaza, wanda ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana a matsayin Wissam Muhammad Sabir al-Saadi, wanda aka fi sani da Abu Baqir al-Saadi.
"Wannan kwamandan shi ke da alhakin kitsa da kuma hannu a hare-haren da ake kai wa sojojin Amurka a yankin."
"Mun fadi cewa kungiyoyin da ke kiran kansu 'yan gwagwarmayar Islama a Iraki su daina kai hare-hare kan dakarunmu da na hadin gwiwa."
“A saboda haka, idan muka ci gaba da ganin barazana da hare-hare daga wadannan kungiyoyin mayakan, za mu mayar da martani; za mu dauki matakan da suka dace.”
"Amurka za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kare jama'arta."
"Kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wadanda ke barazana ga tsaron sojojinta."
Dandalin Mu Tattauna