Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN AMURKA: Har Yanzu Babu Alamun Kawo Karshen Rikicin Syria


Mayakan IS (AP)
Mayakan IS (AP)

Babu wata tabbatacciyar hanyar tsagaita wuta a siyasance da kuma sasanta rikicin siyasa a Syria, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, kuma rashin samun maslaha a siyasance akan yakin basasar kasar ya bar kasar cikin "rikicin kare hakkokin jama’a."

WASHINGTON, D. C. - Kimanin mutane miliyan 7 ne suka rasa matsugunansu a cikin Syria, yayin da miliyoyin wasu ke zama a kasashe makwabta a matsayin ‘yan gudun hijira.

Wani ci gaba mai kyau da aka samu shine tsawaita wa’adin barin mashigar Bab al-Salam da Al Ra'ee a buɗe har zuwa 13 ga watan Agusta, a halin yanzu sune kadai hanyoyin kai agajin jinkai ga mutane miliyan 4.1 a arewa maso yammacin Syria.

Akwai kuma yiyuwar a tsawaita wa’adin amfani da mashigar Bab al-Hawa. Amma dole ne a sake ba da izinin bude hanyoyin akai-akai, lamarin da ke haifar da rashin tabbas yana kuma kawo cikas a yin shiri na lokaci mai tsawo a ta ɓangaren hukumomin agaji.

"Amurka na nan akan kudurinta na samar da agajin jinkai ga Majalisar Dinkin Duniya, ciki har da ta hanyar kan iyaka da kuma hanyoyin ketarawa a Syria. Mun yi alkawarin ba da dala miliyan 593 don wannan kokarin,” a cewar Linda Thomas-Greenfield, Wakiliyar Amurka ta dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.

"A lokaci guda kuma, mun bayyana a karara cewa sake ba da izinin ci gaba da amfani da mashigar Bab al-Salam da al-Ra'ee a cikin karin kwanaki 90 ba abu ne mai dorewa ba don magance girman bukatun jinkai a Syria."

"Muna sake jaddada kiranmu ga gwamnatin Syria da ta ba Majalisar Dinkin Duniya wa’adi mai tsawo na bari a bi ta mashigar Bab al-Hawa zuwa cikin kasar, kafin wa'adin watanni shida da aka gindaya ya kare a watan Yuli. Bai kamata a bar ‘yan Syria suna fama da matsi ba a 'yan watanni."

Ambasada Thomas-Greenfield ta ce "ganin mummunan halin jinkai da ake fama da shi a Syria, da take hakkokin bil-Adama, da rashin tuhumar laifukan gwamnati da cin zarafin da aka aikata, shi ya sa 'yan gudun hijirar Syria suka yi imanin cewa ba za su iya komawa kasarsu ba."

“A bayyane yake cewa gwamnatin Syria ba ta samar da yanayin da zai sa ‘yan gudun hijirar su koma kasar ba a bisa radin kansu kuma a mutunce. Har yanzu ba ta ba da tabbacin kai agajin jinkai ba ko kawo karshen ayyukanta na badda mutane, tsare mutane na rashin adalci, azabtarwa, da kisa.

Har yanzu ba ta fayyace matsayin mutanen da suka bace ba ko kuma ta dakatar da daukar mayaka na tilas. Kuma har yanzu ba ta mutunta haƙƙoƙin da suka shafi gidaje, filaye, da kadarori.”

Ambasada Thomas-Greenfield ta ce, "Lokaci ya yi da ya kamata gwamnatin ta kawo karshen rashin amincewarta, ta kuma yi aiki tare da 'yan adawa bilhakki da gaske don cimma yarjejeniya ta ciyar da daukacin kasar Siriya gaba."

"Amurka za ta ci gaba da ba da goyon baya ga kokarin da ake yi na hukunta gwamnatin Assad akan ta'asar da ta aikata, kuma Amurka za ta ci gaba da jagorantar bayar da taimako ga al'ummar Siriya."

Wannan shi ne sharhin Muryar Amurka da ke bayyana ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG