A ranar 6 ga watan Maris, 'yan sanda sun kai samame ofishin tashar talabijin din Toplum dake watsa labaranta ta yanar, ta kuma tsare 'yan jarida kusan goma sha biyu da ke aiki a wurin. Daga baya an rufe ofishin na Toplum. Har ila yau, a wannan ranar rahotanni sun ce 'yan sanda sun tsare wasu mambobin Third Republic Platform. An kuma tsare mambobin kungiyar masu fafutukar tabbatar da dimokradiyya ta NIDA.
An sako da yawa daga cikin 'yan jarida da masu fafutukar kare hakkin jama'a da aka tsare da tsakar dare, amma har yanzu sauran na tsare a hannun 'yan sanda.
Khadija Ismayilova, babbar Editar kafar Toplum TV sananniyar ‘yar jarida ce mai binciken kwakwaf, kuma tsohuwar shugabar ofishin Rediyo Free Europe/Radio Liberty. Ita kanta Ismayilova ta fuskanci muzgunawa, bayan haka gwamnatin Aliyev ta daure ta a gidan yari tare da tuhumar ta da laifuka marasa tushe saboda rahotannin da ta bada kan cin hanci da rashawa a matakin koli na gwamnatin. Da take tsokaci game da farmakin da kuma tsare mutane na baya-bayan nan, Ismayilova ta ce, “Babu hujja ta kwarai akan abin da ke faruwa. Da alama hukumomi na son su kawar da kafafen yada labarai masu zaman kansu a cikin kasar don dakile wata kafa da za ta dinga ba da damar bayyana ra’ayoyin suka. Babu wani abu da mu ka yi da ya sabawa doka.”
Kudurin hukumomi na murkushe kafafen yada labarai masu zaman kansu ga dukkan alama na kara tsananta a ‘yan watannin nan. Tun a watan Nuwamba gwamnatin Aliyev ta tsare ’yan jarida da dama da ake ganin suna sukar gwamnati, ta kuma kira wasu domin amsa tambayoyi. Daga cikinsu har da shugabannin Abzas Media, wata kafar yada labarai mai zaman kanta mai yaki da cin hanci da rashawa. An kuma auna fitattun mambobin kungiyoyin farar hula.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce Amurka ta damu matuka akan rahoton kama 'yan jarida masu zaman kansu da masu fafutukar kare hakkin jama'a a Azerbaijan a baya-bayan nan.
“Dole ne mu bayyana rashin amincewarmu da yunkurin ci gaba da tsoratarwa, danniya, da hukunta ‘yan jarida, ‘yan gwagwarmayar kare hakkokin jama’a, da ’yan adawa. Muna kira ga Azerbaijan da ta kawo karshen musgunawar da take yi wa wadanda ke amfani da ‘yancinsu, muna kuma kira da a sako duk mutanen da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba saboda dalilan siyasa.”
"Babu wanda ya kamata ya fuskanci dauri a kurkuku ko wani hukunci don ya bayyana albarkacin bakinsa."
Dandalin Mu Tattauna