Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN MURYAR AMURKA: Amurka Ta Himmatu Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Iraki


Unami
Unami

"Amurka ta  himmatu wajen yin aiki tare da gwamnatin Iraki don karfafa, tare da zurfafa dadadden kawancen kasashenmu don neman tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali, da ikon kasar Iraki."

"Sai dai abin takaici, kungiyoyin mayaka masu alaka da Iran na barazanar lalata nasarorin da kasar Iraki ta samu tun bayan fatattakar 'yan ISIS/Da'esh a yankin shekaru bakwai da suka gabata."

"Tun daga watan Oktoban 2023, waɗannan ƙungiyoyin sun kai hari kan sojojin Amurka da na haɗin gwiwa a Iraki, Siriya, da Jordan fiye da lokuta 165."

"Abin takaici, an kashe sojojin Amurka uku tare da jikkata wasu da dama a ranar 28 ga watan Janairu a lokacin da kungiyoyin mayaka masu alaka da Iran suka kai hari kan sojojin Amurka da ke Jordan domin su taka rawa a yaki da 'yan ISIS."

“Wannan asarar mai zafi ce. Ba abun da za mu yarda da shi ba ne. Kuma ba zai yiwu a ci gaba da kai irin wadannan hare-haren ba."

Ofishin ba da tallafi na Majalisar Dinkin Duniya na Iraki, ko UNAMI, har yanzu na da sauran muhimmin aiki a gaba.

Amurka na karfafa ofishin UNAMI don ta taimaka wa hukumar zaben Iraki mai zaman kanta don shirya zaben 'yan majalisar dokokin yankin Kurdawa da na Iraki a karshen wannan bazarar ba tare da bata lokaci ba.

"Muna kuma karfafa gwiwar ofishin UNAMI akan taimakawa gwamnatin Iraki a kokarinta na kare hakkin bil'adama da kuma yaki da rashin hukunta masu aikata laifuka."

A matsayinta na kasar kawancemu a yankin, Amurka na fatan ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Iraki wajen samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG