Anji wani jami’in hukumar zaben Misra a yau Alhamis yana cewa sakamakon zaben da tun farko aka shirya bayyanawa ran Alhamis an sake dagawa har zuwa gobe Juma’a.
Babban jami’in hukumar zaben ta Misra yana mai cewa babban dalilin jinkirin shine ganin yadda har yanzu ba’a kammala kidaya kuri’un zagayen farko na zaben ‘yan majalisar wakilai ba.
Tun farko an shirya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a mazabun birnin Alkahira, da Alxandria da wasu mazabu bakwai ran laraba, amma sai hakan bai samu ba. Wannan zabe shine irinsa na farko a Misra tun hambaras da shugaba Hosni Mubarak a watan Fabarairun da ya gabata. Ga dukkan alamu, hadin gwiwar kungiyar Muslim Brotherhood da sauran jam’iyyun ra’ayin rikau karkashin Inuwar jam’iyyar al-Nour Salafi ne zasu sami gagarumar nasara a zaben Majalisar dokokin na kasar Misra.