Bangarorin da ke yaki da juna a Sudan sun amince da wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa’a 72.
Hakan na faruwa ne yayin da kasashen turai, larabawa, Asiya da na Afirka ke ta kwashe mutanensu a kasar.
Dakarun Sudan sun ce Amurka da Saudiyya ne suka shiga tsakani aka cimma wannan matsaya ta tsagaita wuta wacce ta fara aiki da tsakar daren Litinin.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a ranar Litinin ya ce, kulla yarjejeniyar ta biyo bayan kwana biyu da aka kwashe ana kokarin sasantawa.
Dakarun Sudan da abokanan hamayyarsu na SRF da ke gwabza fada a kasar, sun sha karya yarjejeniyoyin tsagaita wuta da aka cimma a makon da ya gabata.
“A wannan karon, Amurka na kira ga bangarorin dakarun SAF da na SRF, da su mutunta wannan yarjejeniya.’ Blinkne ya ce.
Fada ya kaure ne tsakanin bangarorin biyu a ranar 15 ga watan Afrilu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 427.