Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta kafa wani kwamiti da zai shirya yadda za a yi jigilar ‘yan Najeriya daga Sudan da ke fama da rikici
Wata sanarwa da Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta NEMA ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Manzo Ezekiel, ce ta bayyana kafa kwamitin kamar yadda Channels ya ruwaito.
Kasashen Birtaniya, China, Amurka Saudiyya da sauran kasashen duniya na ta yunkurin ganin yadda za su kwashe ‘yan kasarsu.
A ranar Asabar Suadiyya ta yi nasarar kwashe mutum 50.
A makon da ya gabata ne, kasar ta Sudan da ke Arewacin Afirka ta tsunduma cikin rikicin tsakanin dakarun kasar da wasu mayaka masu sanye da kayan sarki da ake kira RSF.
Kafa wannan kwamiti da hukumomin Najeriya suka yi, shi ne mataki na baya-bayan da kasar ta dauka, kasa da sa’a 24 bayan da gwamnati ta ce babu halin da za a yi jigilar saboda yanayi na rashin tsaro musamman a yankin filin tashin jirgin Khartoum
Sai dai a ranar Asabar NEMA ta ce kwamitin na dauke da kwararru a fannonin ba da agajin gaggawa, da kuma bincike da kubutarwa.
Hukumar ta NEMI ta kuma kara da cewa, tana ci gaba da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki kan lamarin tare da tattara bayanan da suka dace.