Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Rikicin Sudan Ya Shafi Harkokin Kasuwacin Kasar Da Nijar


Yadda masu manyan motoci suka danse hanya a Neja
Yadda masu manyan motoci suka danse hanya a Neja

Rikicin kasar Sudan ya saka direbobi da mamallakan motocin da ke jigilar kayayyakin kasuwaci daga jihar Diffa ta Jamhuriyyar Nijar zuwa kasar ta Sudan a cikin yanayi na zullumi.

A yanzu haka manyan motoci da dama suka yi lodi a jihar ta Diffa amma suka kasa dagawa zuwa kasar ta Sudan sakamakon wannan rikici.

Fiye dai da mako daya ke nan da kasar Sudan ta fada a cikin wannan rikici, inda ake musayar wuta tsakanin sojojin Sudan a karkashin jagorancin Janar Aldulfatah Alburhan da sojojin RSF da ke karkashin jagorancin Mohammed Hamdan da ma wasu ‘yan tawaye da ba su yi fice ba.

Tuni dai wannan rikici ya fara shafar hada-hadar kasuwanci tsakanin kasar ta Sudan da wasu kasashen Afirka, alal misali, jihar Diffa ta jamhuriyyar Nijar ta kasance jihar da wasu kasahen Afirka irin Chadi da ma wasu yankunan Nijar ke amfani da ita wajen shigar da kayayyakin kasuwancinsu a kasar ta Sudan.

Kwanaki goma ke nan da al’ummuran zirga-zirga ke tafiyar hawainiya tsakanin jihar ta Diffa da kasar ta Sudan, al’amarin da ya jefa direbobi da kuma ‘yan kasuwar da ke shigar da kayayyakin kasuwancinsu a kasar ta Sudan a cikin wani hali na tsaka mai wuya.

Kafin dai barkewar wannan rikici a kowane mako ana samun akalla tireloli biyar zuwa shida da ke loda kayayyakin kasuwanci daga jihar ta Diffa zuwa kasar ta Sudan.

To amma barkewar wannan rikicin ya hana motoci da dama da suka yi lodi a jihar ta Diffa zuwa kasar ta Sudan soboda fargabar.

A hirar shi da Muryar Amurka, Adam Aboubakar, direba ne kuma dan kasar Sudan, ya ce sun shiga cikin matsala sosai don tun lokacin da wannan rikici ya barke direbobi da masu kaya duka suna cikin wahala, daga Chadi, Nijar da Sudan kuma a cikin wannan ne suke cin abincinsu.

Ya kuma yi kira da a taya su da addu’a wannan fitinar Allah ya tsayar da ita haka.

Shugaban Kungiyar Manyan Motoci Na Nijar, Kiari Amoutapha, ya bayyana damuwarsu game da wannan al’amari na kasar Sudan, inda ya ce direbobinsu dake zuwa tun da aka fara rikicin sun janye motocinsu.

Sai dai a lokacin hada wannan rahoto duk kokarin jin ta bakin ‘yan kasuwar Nijar da suka kasa shigar da kayayyakin kasuwancin nasu a kasar ta Sudan sakamako wannan rikicin yaci tura.

Saurari cikakken rahoton Aboukar Issa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG