Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Kwashe Jami'an Jakadancin Nijar Daga Sudan Ya Haifar Da Dambarwa


An kwashe wasu daga Sudan zuwa Spain
An kwashe wasu daga Sudan zuwa Spain

Gwamnatin Nijar ta ce ta samu nasarar kwashe jami’an diflomasiyyarta daga Sudan zuwa Djibouti a wani kokarin hadin gwiwa da kasar Faransa, sai dai wasu ‘yan kare hakkokin bil’adama na ganin ba a yi wa dalibai da sauran ‘yan Nijar mazauna Sudan adalci ba saboda yadda aka bar su a Khartoum.

A sanarwar da ta fitar da sanyin safiyar Laraba 25 ga watan Afrilun 2023 wacce aka aike wa manema labarai, ma’aikatar ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijar ta bayyana farin ciki akan abinda ta kira samun nasarar kwashe jami’anta daga Sudan su kimanin 38 da suka tsallaka kasar Djibouti da taimakon dakaru na musamman da ake kira Forces Speciales na kasar Faransa.

Gwamnatin Nijar ce ta tuntubi ofisoshin jakadancin Faransa a Khartoum da Yamai akan bukatar bai wa wadannan jami’ai damar shiga ayarin ‘yan Faransa da aka kwashe daga Khartoum a cewar sanarwar.

Arewacin Khartoum
Arewacin Khartoum

Shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou, da ke bayyana ra’ayinsa, ya yaba da wannan mataki da ya ke kallo a matsayin wata alama ta kyakkyawar huldar kasashen biyu.

Ko da yake babu wasu alkaluma na hakika a hukumance dangane da yawan ‘yan Nijar mazauna Sudan, wasu majiyoyi na kwatanta cewa miliyoyi ne ke rayuwa a wannan kasa ta yankin gabashin Afrika haka kuma akwai dalibai ‘yan Nijar da ke karatu a jami’o’in Sudan, abinda ya sa shugaban kungiyar Kulawa da Rayuwa Hamidou Sidi Fody, ke nuna damuwa a kan halin maraicin da aka bar wadannan bayin Allah a ciki bayan da aka kwashe jami’an jakadancin Nijar daga Khartoum.

Khartoum, Sudan
Khartoum, Sudan

Wannan ya sa Saidou ke shawartar gwamnatin Nijar da ta dage da neman hanyoyin kubutar da sauran ‘yan kasar daga halin tsaka mai wuyar da ake ciki a Khartoum.

A hirar da Muryar Amurka ta yi ta waya da su a yammacin Litinin, dalibai ‘yan Nijar da ke Sudan sun koka a game da abinda suka kira halin ko in kula da jami’an karamin ofishin jakadancin kasar suka nuna a game da halin da suke ciki, akwai lokacin da abinci, da ruwa, da wutar lantarki suka yi wuya sakamakon kazamin fadan da aka shafe kwanaki sama da 10 ana kafsawa a tsakanin janar-janar din da ke hamayyar rike madafun iko.

Saurari rahoton Souley Mumuni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG