Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya Ta Fara Kwashe ‘Yan Kasarta A Sudan

Wasu 'yan kasashe da suka biyo jirgin Saudiyya da ya fara jigilar kwaso 'yan kasa a Sudan da ke fama da rikici.
Wasu 'yan kasashe da suka biyo jirgin Saudiyya da ya fara jigilar kwaso 'yan kasa a Sudan da ke fama da rikici.

A ranar Asabar an yi ta barin wuta yayin da jiragen yaki ke tashawagi a sararin samaniyar Khartoum a cewar shaidu.

Wani jirgin ruwa dauke da ‘yan kasar Saudiyya da wasu ‘yan kasashe daga Sudan, ya isa birnin Jidda a cewar wani gidan talbijin din kasar.

Jirgin ya yada zango ne a tashar jirgin Jidda inda ake sa ran wasu jirage hudu dauke da mutum 108 su ma za su isa tashar.

Sauran jiragen hudu da ake sa ran za su isa, na dauke ne da wasu ‘yan kasashe 11.

“Jirgin na dauke da ‘yan Saudiyya 50 da wasu ‘yan kasashe da ke kawance da Saudiyya.” Gidan talbijin din Ekhbariyah ya ce.

A ranar Asabar an yi ta barin wuta yayin da jiragen yaki ke tashawagi a sararin samaniyar Khartoum a cewar shaidu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG