Yarbawan sun baiwa Fulani wa'adin ne sakamakon zargin cewa su Fulani ne suka yi garkuwa da tsohon sakataren gwamnantin tarayyar Najeriya Chief Olu Falae.
Alhaji Muhammad Kirwa Ardon Zuru shugaban kungiyar Fulani ta Najeriya wato Miyetti Allah yace babban martanin da suke son su maida suna son Yarbawa su sani Olu Falae ba shugaban Yarbawa ba ne kawai. Ya taba zama sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya kuma ya mulki kowace kabila a Najeriya.
Batun koro wani daga kudu zuwa arewa ba zai haifar wa kasar da mai ido ba, inji Alhaji Kirwa. Yace yanzu tunanen Najeriya shi ne dinke barakar da ta taso a wasu wurare saboda a samu zaman lafiya.
Gwamnatin yanzu kokari ta keyi ta samar ma kasar zaman lafiya.
Dattijon Fulani Muhammad Dodo Oroji ya kira majalisar kasa ta yi wani abu. Yace abun da a keyi a Najeriya abun takaici ne. Yace duk dan Najeriya na iya zama inda ya ga dama. Ya kira masu ikon kasar su hukunta duk wani wanda zai yi irin kalamun da Yarbawa suka yi.
Kwararre a harkokin tsaro Birgediya Sale Bala mai ritaya yace akwai mafita. Yace Najeriya ta zama kasarmu gaba daya. Ya kamata a manta da batun kabilanci ko bangaranci ko addini. Kowa na iya zama inda ya ga dama amma dole ne ya mutunta al'ada da akidar mutanen da ya je ya zauna cikinsu. Yace saboda haka a dinga yin furucin da zai hada kawunan 'yan kasar. Yarbawa da 'yan arewa sun dade suna tare kuma babu wanda ya fi Yarbawa jin dadin saniya. Inji Sale Bala abu ne da ya faru amma ba'a yi zurfin tunane a kansa ba.
Matakin da majalisar waikai ta dauka jiya tamkar mayarda martani ga takaddamar dake tsakanin Yarbawa da Fulani a kudancin kasar ne. Majalisar ta umurci gwamnatin tarayya ta yiwa Fulani makiyaya burtuloli domin magance yawan rigingimu tsakanin makiyaya da manoma da yanzu ya mamaye jihohin arewa kuma yana neman ya kai kuduancin kasar
Ga karin bayani.