A makon jiya ne dai wasu ‘yan bindiga da akayi zargin ko Fulani ne suka afkawa garuruwan Alawa da kuma kwanar Mariga, inda suka kashe jama’ar garin da dama ciki kuwa harda hakimin garin da kuma shugaban yan sandan yankin, a wani al’amari da ake ganin na ramuwar gayya ne a sakamakon wasu Fulani da aka taba kashewa a garuruwan, a dalilin zarginsu da ake da zama cikin ‘yan fashi.
Lokacin taron manema labarai mataimakin shugaban kungiyar Miyatti Allah a Najeriya Alhaji Husaini Boso, ya nesanta kungiyar sa daga wadannan hare-hare inda yace, “baruwanmu da wannan harin, idan Fulanine ma suka aikata to mu mun daukesu a matsayin masu barna, domin duk wanda yace zai rama abinda akayi masa to ya nuna babu doka a kasa.”
Alhaji Husaini Boso, ya tabbatar da cewa kungiyar ta kaddamar da wani shiri na wayar da kan fulanin musammam ma matasa akan illar tayar da zaune tsaye.
A bangaren shugaban rikon kungiyar Alhaji Adamu Kaduna Tsauni, ya bukaci jama’a da su daina daukar doka a hannunsu idan al’amari ya faru. Ya kuma bayyana bukatar ganin hukumomi sun samar da daji domin kiwon dabbobinsu.
Duk da cewa daruruwan jama’a sun kauracewa yankin na Alawa, hukumomin tsaro sunce sun kara tura jami’an su a yankin domin tabbatar da doka da zaman lafiya.