Kungiyar da yanzu take karkashin Ardon Zuru ta nesanta kanta da alaka da kowace jam'iyyar siyasa a Najeriya.
Matsayin da Miyetti Allahn ta dauka ba zai rasa nasaba da fitowar da kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore tayi da nuna Fulani na marawa shugaba Jonathan baya ya zarce.
Baba Usman Ganjarma sakataren Miyetti Allah na kasa kungiyarsu ita ce kowane Bafullatani ya sani a Najeriya. Miyetti Allah Kautal Hore da ta shiga harakar siyasa su basu da alaka da ita. Kuma suna Miyetti Allah nasu ne ban da haka akwai wata kungiya mai suna Kautal Hore domin haka an dauki sunayen biyu an hadasu aka yi anfani dasu tamkar kungiya daya domin jawo rudani.
Ya kira Fulani su sani cewa Miyetti Allah ta kasa ba kungiya ba ce da aka ginata kan manufofin siyasa ba. Kungiya ce da aka ginata kan manufofin kare muradun Fulani da kuma kiyaye hakinsu a duk inda suke a kasar. Iyayen kungiyar kamar Sarkin Musulmi da wasu sarakunan arewa tun lokacin da aka kirkirota su ne iyaye.
Dattijon kungiyar Dodo Oroji ya gano wasu daga cikin kalubalen dake fuskantar kungiyar. Sun kira gwamnati a sabunta burtololin da aka san inda suke. Kowace jiha ta kebe wuraren kiwo. A kebe gandayen daji.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.